Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) a Jihar Kano, ta bayar da shawarar tilasta yin gwajin ƙwayoyi ga ma’auratan a wani mataki na rage shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar.
Kwamandan NDLEA a Kano, Mista Abubakar Idris-Ahmad ne, ya bayyana haka inda ya ce gwajin ƙwayoyin zai zama wani mataki na rigakafin shan muggan kwayoyi da kuma gano ko ma’aurata suna ta’ammali da miyagun ƙwayoyi domin samun magani da gyara da ya dace.
Ya ce akwai buƙatar dokar da aka tsara na gwajin domin magance yawaitar matsalar auratayya da kuma rage shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin ma’auratan.
Ya yi kira ga majalisar dokokin jihar, da ta samar da dokar da za ta buƙaci a yi gwajin miyagun ƙwayoyi kafin aure.
Kwamandan, ya yi kira ga mata da matasa da sauran jama’a da su guji shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da haɗa kai domin ciyar da jihar da ƙasa gaba.
Leadership Hausa