Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeIlimiJami’ar Yar’adua Da Ke Katsina Na Dab Da Durƙushewa – ASUU

Jami’ar Yar’adua Da Ke Katsina Na Dab Da Durƙushewa – ASUU

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ta kama hanyar rugujewa sakamakon rashin isassun kuɗaɗen gudanarwa daga gwamnatin jihar.

Shugaban ƙungiyar Malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshen UMYUK Dakta Murtala Abdu Kwara ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Katsina.

Ya ƙara da cewa maganar da ake yanzu jami’ar na kokowa da matsalar rashin wadatattun kuɗaɗen gudanar da ɓangaren ma’aikata da kuma ɗalibai.

A cewar Dakta Murtala Abdu Kwara gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa na ba wa jami’ar Naira miliyan ₦7m duk wata a matsayin kuɗin gudanarwa a maimakon miliyan 16 da ake bata a gwamantin da ta gabata.

Wannan jami’a ta fara karatu ne da tsangaya uku ne kacal da kuɗin gudanarwarta miliyan 16, yanzu kuma muna da tsangaya 9 amma kuɗin gudanarwa ba su canza ba, suna nan miliyan 7″ inji shi

Ya ce halin da jami’ar take ciki a halin yanzu ta sa dole aka dakatar da baiwa sassan jami’ar kuɗaɗen gudanarwa.

Haka kuma ya koka kan yadda gwaman Dikko Umar Raɗɗa ya ƙi aiwatar da kaso 25/35 na albashin ma’aikata wanda ya ce wasu jami’o’i tuni sun fara aiwatarwa.

Kazalika Dakta Murtala Abdu Kwara ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina ta sake duba tsarin biyan kuɗaɗen gudanarwa na jami’ar domin ceto ta daga durƙushewa.

Duk wani ƙoƙari domin jin martani daga bakin Kwamishin ma’aikatar ilimi mai zurfi na jihar Katsina Farfesa Abdul Hamid Ahmad ya ci tura kafin kammala haɗa rahoton.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments