Kano gari ne mai dumbin tarihin asali, ilimi da tattalin arziki, duk wanda ya san Kano shekaru 25 kawai a baya zai iya tuno yadda karamci da dattaku da karbar baki yake a ko ina a garin Kano. A shekarar 2000 na taba shigowa mota daga Katsina na iso Kano cikin dare zan wuce Maiduguri, a mota mu ka hadu da wani bakane, yace mun dare yayi mu je gidan su mu kwana, kuma dalili kenan na je har mu ka saba da mahaifiyar shi sosai sosai.
Amma gaskiya a halin yanzu ina tausayin Kano da Kanawa, domin ya’yan su matasa ba za su mori irin wannan halaye ba, domin gurbacewar tarbiyya da aka shigo musu da ita. Mutane da dama sun kwararo Kano da munanan dabi’un su, kuma sannu a hankali suna tasiri a rayuwar matasan su. Har ta kai ga matsayin duk wani mai daraja ko dauka sarki ne ko malami, dan siyasa ne ko dan kasuwa, bai fi karfin a ci mutumcin shi a gidan radio ba.
Gari ne guda daya, amma gidajen radio kusan 40, kowa yana ta surutu da maganganu iri-iri. Sannan ga wasu yan siyasa suna kara tunzura abun saboda siyasar su, sannan wasu malamai ma suna amfani da wannan dama domin samun mabiya su yi ta maganganu, bugu da kari ga zaizayewar tattalin arziki da yake jawo kunci da rashin jin dadin rayuwa.
Ina kira ga sabbin dattawa yan’uwa na a jihar Kano, da su tashi su tsaya sosai akan abujda ya shafi tarbiyar ya’yan mu, kar su bari wasu mutane su lalata musu tarbiya sabosa son rai, ko rashin asali dss.
Ra’ayin Sharif Almuhajir