‘Yan ta’adda sun kai harin ramuwar gayya cikin dare a ƙaramar hukumar Danmusa.
Bayan da jami’an tsaro suka hallaka ‘Yanbindaga da dama a kan hanyar zuwa garin Maidabino da ke ƙaramar hukumar Danmusa, ‘yanbindigar sun yo taron dangi a sassa daban-daban inda suka shigo cikin garin su ka yi ɓarna mai tarin yawa.
Sai dai, an zargi wani babban Ɗanta’adda da ke jihar Zamfara wato Buzaru da jagorantar harin.
‘Yan ta’addar sun kashe mutane da dama a garin da kuma sun ƙone motoci a garin wanda har yanzu wakilin Katsina Post bai samu tabbacin ko Mota nawa ce aka ƙone ba.
Tunda farko, ‘yanbindigar sun yi ayari kan hanyar daga ‘Yantumaki zuwa Maidabino a marecen ranar Juma’a 21 ga watan Yuni, 2024, inda suka hana ‘yankasuwar komawa gida bayan sun kammala cin kasuwa.
Majiyar ta ce, da jin hakan sai jami’an tsaro su ka yi shiri na musamman domin kare al’ummar da kuma raka su zuwa garin su, inda a kan hanyar suka yi galaba a kan ‘yanbindigar tare da kashe su da dama a safiyar jiya Asabar.
Majiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya jaddada cewar ‘yanbindigar sun yo hayar abokan su daga jihar Zamfara domin ramuwar gayya a garin Maidabino ta ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina.
Ya ce ana zargin wani babban Ɗan’adda daga jihar Zamfara mai suna Buzaru da jagorantar ta’addancin, a cewar sa, tun a daren jiya da misalin ƙarfe 7 na dare suke ta’addanci a garin wanda suka kai kimanin awannin 2 zuwa 3 ba su daina ba.
A yayin haɗa wannan rahoton, ba mu samu tabbacin ko Mutane nawa ne aka kashe a garin ba, saide mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, amma abin yaci tura, amma mun aika ma sa da saƙo ta wayar salula, inda ya maido da saƙon an kashe mutane 7.
Kazalika, a cikin saƙon ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan lamarin, kuma duk bayyanan da suka ƙara samu za su sanar nan ba da jimawa ba.